Kannywood
RARARA YA GWANGWANJE WANI DATTIJO DA KYAUTAR SABON BABUR
RARARA YA GWANGWANJE WANI DATTIJO DA KYAUTAR SABON BABUR
Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ba wani Dattijo mai suna Abdullahi Ɗan Jarida, da ke ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar, a jihar Jigawa kyautar sabon mashin (Roba Roba)
Shugaban kamfanin Al-Hikima Islamic Medicine, Dr. Abdullahi Haruna ne ya jagoranci bada kyautar.
Dattijon, ya kasance ɗaya daga cikin masoyan Rarara, wanda lokaci bayan lokaci ake ganin shi yana hawan wakokin Rarara a shafin TikTok.
Wane fata zaku yi masa?