Rawar Iskancin Safara’u / 442 Yana Cikin Mawuyacin Hali A Kurkukun Niger
Bayyanar Wani video iskanci Safara’u ya Jawo Cece Kuce 442 yana cikin Wani mawuyacin Hali a Kurkukun Niger.
Kamar yadda ka sani dai a yanzu haka an kama 442 da abokin sa ola kamar yadda a yanzu haka suna Kurkuku a Kasar Niger Inda a yanzu haka mutane da yawa Suna magana akai.
Gadai Bidiyon
A yanzu haka kuma mutane da yawa Suna magana akan cewa ya kamata a Sakasu amma kuma a yanzu haka a dokara kasar Niger bada bada damar Sakin su ba.
A yanzu haka ga Video ka kalla domin zakaji yadda wannan labarin ya ke Akan kama 442 kuma a yanzu haka indai ka kalli wannan Video Zakaji Bayani akai.
Sabbin Dokokin Hada-hadar Kuɗi A Nijeriya
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Sabbin dokokin zasu fara aiki ne a watan ɗaya na sabuwar shekara (9/01/2023)
Ga dokokin kamar haka:
1. Duk wanda zai cire kuɗi a asusun ATM, iya Naira dubu ashirin (₦20,000) kawai zai iya cirewa a rana.
2. Haka kuma Naira dubu ashirin ce kacal (₦20,000) mutum zai iya cirewa a rana a asusun POS.
3. Naira dubu ɗari ce kacal (₦100,000) mutum zai iya cirewa a ATM ko POS a cikin sati daya.
4. Mafi girman kuɗin Naira za za’a dinga sakawa a dukkanin ATM itace Naira ɗari biyu (₦200).
5. Mafi yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a cikin banki wato Counter a wuni shine Naira dubu ɗari (₦100,000).
6. Idan kuma wata ma’aikata ce zata cire kuɗin a cikin banki wato Counter, mafi yawan kuɗin da za’a iya cira shine Naira dubu ɗari biyar (₦500,000).
7. Dukkanin kudaden da aka samu dalilin mai karfi na fitar da sama da abinda doka ta amince dashi, Tou za’a biya kuɗin processing fee na cirar waɗannan kudaden.
Idan mutum ne zai cire sama da adadin ba kamfani ko ma’aikata ba, zai biya kudin kamisho wato processing fee na kashi biyar cikin dari da adadin kudin da zai cire wato 5%.
Idan kuma kamfani ne ko ma’aikata, zasu biya kudin kamisho wato processing fee na kashi goma cikin ɗari wato 10% na abinda zai cire.
8. Dukkanin kuɗin da za’a cire ta hanyar wani ya baka Cheque wato 3rd Party Cheque na kudin da ya haura Naira dubu hamsin (₦50,000) dole sai a counter za’a cire.
Wadannan wasu ne daga cikin sabbin dokokin hada-hadar kuɗi da bankin CBN ya fitar.
Zamu kawo dalilan kafa waɗannan sabbin dokokin hada-hadar kuɗin na Nijeriya insha Allahu.