Labaran duniya

Saraunìyar Ingìla Queen Elizabeth Ta Fí Wasu Musulmaí Musulunci Kuma Ina Mata Zaton Shiga Aljannah, Cewar Adamu Garba

FAHIMTA FUSKA!

Saraunìyar Ingìla Queen Elizabeth Ta Fí Wasu Musulmaí Kuma Ina Mata Zaton Shiga Aljannah, Cewar Adamu Garba

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Nijeriya a jam’iyyar #YPP Adamu Garba, ya wallafa wani rubutu da bidiyo da ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta na zamani.

Adamu ya yi rubutu ne cewar ya yi mafarkin marigayiya Sarauniyar Ingila tana sh@ƙatawa a cikin Aljannah Firdaus, sannan ya wallafa wani bìdìyón inda yake bayyana cewar tafi wasu musulmaí.

“Yanzu na yi mafarki Queen Elizabeth tana shaƙatawa a cikin Jannatul Firdaus, Allah ya tabbatar da hakan. Sarauniyar Ingila ta gina masallaci mafi girma a Landan, kuma ta fí wasu musulmaí, kuma ina yi mata zaton shiga Aljannah.” Inji Adamu

Hakan yasa mutane da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu game da wannan kalamai nasa, inda wasu ma suka buƙaci Malamai su zauna da shi domin warwarewa al’umma wannan al’amari.

Ku bayyana mana ra’ayoyinku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN