Labaran duniya

Shekara Ashirin Kenan Ba Na Shan Ruwa Kuma Ina Yin Rayuwata Cikin Kwanciyar Hankali

Shekara Ashirin Kenan Ba Na Shan Ruwa Kuma Ina Yin Rayuwata Cikin Kwanciyar Hankali, Cewar Rastafari (Rastaman)

Wani mutum mai suna Karton Rastafari wanda akewa laƙabi da Rastaman ɗan ƙasar Burindi, ya bayyana cewar shekarunsa 20 ba tare da ya sha ruwa ba.

Rastaman ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da ƴan uwansa.

“Na daina shan ruwa ne tun shekaru 20 kuma ina gabatar da rayuwata a cikin kwanciyar hankali kamar sauran mutane.” Inji shi

Sai dai Rastaman bai bayyanawa ƴan uwan nasa dalilinsa na yin hakan ba, ya dai shaida musu cewar ya daina shan ruwan ne ba tare da wani dalili ba.

Hakan ya al’umma cikin mamaki da cece-kuce ganin yadda ruwa yake da matuƙar amfani ga rayuwa, domin da shi kowanne mai rai ke rayuwa, amma shi Rastaman ya bayyana cewar yana gabatar da rayuwansa ne ba tare da ya sha ruwa ba.

©Idon Mikiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN