Shine Bidiyon yadda aka Kăshèè Mana Bayin Allah a yayin da suke Maulidi Manzon Allah S.A.W a kaduna
Allah Sarki Rayuwa😭, Shine Bidiyon yadda aka Kăshèè Mana Bayin Allah a yayin da suke Maulidi Manzon Allah S.A.W a kaduna.
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN !!!
Kamar yadda Muka wayi gari da Mugun Labari Mai Tayar da Hankali Mai Bata Rai, Mai dauke da alamomin Tambaya yau a Nigeria
Tada BOM akan Musulmin da basu ji ba basu gani ba, da Sunan Kuskure yayin da Suke Raya dare da Ambaton Annabi saww da yabonsa
Wannan ya faru ne a Tudun Biri dake gundumar afaka, Karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna Wanda ya daure Kai matukar yabada Mamaki
GADAI BIDIYON ANAN
▶️ PLAY
Koda yake Rundunar Soja ta dauki Alhakin harin da Sunan Kuskure kamar yadda BBC ta ruwaita, Gwamna Jihar Kuma ya bayar da Umurnin yin bincike Gaugawa akan LAMARIN
Sai dai Wannan Bai Isa ba, Da farko Wajibi ne Rundunar Soja da Gwamnatin Kaduna su Dauki Nauyi Biyan kudaden Magani da kula da lafiyar wadanda suka Rayu dauke da RAUNUKA
Sannan a biya Diyar dukkan Wadanda suka Rasa Rayukansu Maza da Mata, Kuma a nemi Afuwar ‘Yan uwansu da Masoyansu Musulmi
ZAKU IYA KALLON BIDIYON KAI TSAYE TA NAN
A Kuma Bayyana Sakamakon Binciken Tsakani da Allah batare da Son Zuciya ba, idan akwai Sakaci ko Kuma Ganganci ko Wata 6oyayyar MANUFA a hukunta masu wannan mugun aiki.
Idan ba ‘a ‘yi Wadanan Abubuwa ba, ba a yi Muna Adalci ba, Mu masu Maulidi da sauran Musulmi Kuma bazamu kyale ba, zamu Dauki Matakin Kai KARA ZUWA GA ALLAH TA’,ALAH
Shi kuwa Allah baya Bacci baya Shagala ba Abunda ke 6oyuwa gareshi, baya Zalunci baya Kyale Azzalumai ko me Tsawon dadewa Kuma yayi ALKAWALIN sakawa Wanda aka Zalunta
Wadanda abin abin ya shafa suyi Albishir Shahada a tafarkin Allah ita ce MUTUWA Mafi Daraja, da duk Mai Imani yake NEMA, Sahabbai da yawa sun SHAHADA Fansa ga Annabi saww
Kuma Hakika Annabi saww yace: Wanda aka kashe saboda addininsa yayi SHAHADA don haka ko akan Kuskure ko Sakaci ko Ganganci aka kashe su dai SHAHADA ce, Insha Allah
Allah ya Azurtamu Mutuwar Shahada a Janibin Annabi saww, Muna Ta’aziya ga dukkan Musulmi Musamman iyalan Mamatan, Muna Jajantawa da adduar samun Lafiya ga masu RAUNUKA
MUNA MAIMAITA KIRA GA GWAMNATIN NIGERIA DA TA KADUNA DA RUNDUNAR SOJA NIGERIA A YI BINCIKE AIMANA ADALCI !!!
Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 04/12/23 20-05-1445AH