Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin buɗe iyakokin ƙasar da Nijar nan take.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin buɗe iyakokin ƙasar da Nijar nan take.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duk kanin sauran takunkuman da Nijeriyar ta sanyawa Nijer.
Jerin takunkuman da Najeriya ta bada umarnin cirewa Nijar nan take: –
1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakannin Nijeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.
2- Dakatar da duk kan cinikayya tsakanin Nijeriya da Nijar tare da dakatar da duk kan ayyukan da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.
3- Rike kadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.
4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.
5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea.
Wannan dai na zuwa ne bayan ECOWAS ta cire takunkuman da ta saka wa Nijar a kwanakin baya.