Labaran Kannywood

Tirkashi Ado Gwanja Yayi Zazzafan Martani Ga Lauyan Daya Makashi a Kotu Akan Wakar Chass

Babu wanda ya taba bani sana’a, dan haka babu wanda ya isa ya hana ni sana’a ta, ta Waka ~ Ado Gwanja

Fitaccen mawakin Kannywood Ado Isa Gwanja ya maida martani game da karar sa da wani lauya ya kai hukumar Hisba.

Jaridar Amintacciya ta rawaito cewa, Ado Gwanja ya maida martanin ne lokacin da yake zantawa da Freedom Radio, inda aka tambaye shi akan ko me zaice game da karar sa da Lauyan ya kai.

Ado Gwanja ya ce shi Lauya Sana’ar sa yake kuma babu wanda ya hana shi dan haka nima sana’a ta nake.

Ado Gwanja ya cigaba da cewa tun kafin a haife shi ake wakar Asosa dan haka karya ne ace wai wakar sa ce zata rusa tarbiyya.

A karshe yace Sana’a yake, kuma a baya babu wanda ya bashi sana’a dan haka babu wanda ya isa ya hana shi.

Idan baku manta ba mun kawo muku labarin cewa, wani lauya Mai suna Barr. Badamasi Sulaiman Gandu yayi barazanar maka hukumar hisba ta jihar kano a gaban kotu matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin matan nan wato Ado Isa Gwanja daga fitar da wata Sabuwar waka da yayi Mai suna Casss.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN