Tirkashi Maganar Kama Su Ado Gwanja da Safara’u dai ta tabbata Kotu ta bada Umurnin Kamo su
ZARGIN BATA TARBIYA: An Maka Su Ado Gwanja, Mr 442, Safara’u, Murja Da Sauran Wasu Masu Tikar Rawar Badala A Tiktok Bisa Zargin Yada Badala
takarda da kotun majistare dake Bichi, karkashin mai shari’a, Bello Musa Khalid, takarar tace an bukaci kwamishinan dan
sanda na jihar Kano, ya gudanar da bincike akan wadanda ake zargin.
Tunda fari dai lauya Barista Badamasi Sulaiman Gandu Esq, ne ya bada wa’adin kwanaki uku ga hukumomin da abun ya sha fa akan su dauki mataki ga mawakin Ado Gwanja, akan wata sabuwar waka da yayi mai taken “Asosa” wacce ake zargin
anyi amfani da kalaman batsa a cikinta, idan kuma ba haka ba zai garzaya kotu.
Yanzu dai haka lamarin ya karagirmama, domin a cikin kunshin lauyoyin da suka kai wadancan mutane a kotu, bayan Barista
Badamasi, akwai, Barista Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, da kuma G.A Badawi.
Daga Cikin abubuwan da akayi kara akansu sun hada da yinwasu wakoki da sukayi karo da addini da kuma al’ada, masu taken “Warr” da kuma “Chass” wanda Ado Isa Gwanja yayi, sai kuma sauran da ake zarginsu da hawa kan wakoki suna tikar rawa da kuma wasu abubuwa da suka ci karo da addinin musulunci.
Zakuji cikakken bayanin ta hanyar danna hoton bidiyo dake kasa.