Labaran Kannywood

Tofa! An gano cewa Naziru Sarkin Waka Kasurgumin mai yin mining Pi Network ne

RUFE BAKIN TSANYA

Mawaki Naziru Sarkin Waka yana daga cikin mutanen da suke kushe Pi Network, bincike ya gano cewa Naziru Sarkin Waka Kasurgumin mai yin mining Pi Network ne, duka lambobin wayoyinsa guda biyu yana yin Mining Pi da su

Ga binciken da shafin Gonar Pi Network suka gudanar akan Naziru Sarkin Waka

Yadda Mukayi Binciken Ƙwaƙwaf Har Muka Gano Cewa Naziru Sarkin Waƙa Yana Ɗaya Daga Cikin Masu Mining Pi..

Abu Na Farko Mun Nemi Lambarsa Inda Muka Binciketa, Ta #Truecaller Wadda Ta Tabbatar Mana Da Cewa Lambarsace.

Abu Na Biyu Munyi Amfani Da Lambar Ƙarƙashin Application Na Pi Sashen Security Wato (Security Cycle) Inda Ta Tabbata Cewa Naziru Sarkin Waƙa Na Ɗaya Daga Cikin Mutanen da Suke Mining Pi.

Akwai Buƙatar Waɗanda Suke Jin Daɗin Kalaman Da Naziru Sarkin Waƙa Yayi Akan Pioneers Musamman Na Yankin Arewa Su Bibiyi Waɗannan Hotuna Su Gani Su Tabbatar da Cewa duk da tabargazar da Naziru Sarkin Waka yayi akan masu Mining Pi ashe yana Daga Cikin Masu Yin Mining Na Pi👌 ~Gonar Pi sun rufe mana bakin Naziru daga yau

Karin bayanin da zanyi shine hatta nambar wayan BBC Hausa da suke yin WhatsApp dashi ana yin mining Pi, akwai nambar wayoyin wasu daga cikin manyan bankunan Nigeria na Customer care duka mun bincika mun tabbatar ana mining Pi da su, har da nambar wayan wani Gwamna da yake mining na gani, akwai Sanatoci da manyan ‘yan kasuwa wadanda suka san Crypto da Blockchain suna mining Pi

Duk wanda kuka ga ya dage yana sukar Pi to ku nemi nambar wayansa kawai kuyi saving a contact, ku bude application na Pi Network gurin Security zai nuna muku, don haka abin nasu na sukar Pi ba komai bane illa kyashi da hassada sai kuma jahilai wadanda za’a barsu a baya

Allah Ka taimaki Pi Network
Allah Ka tsare mana Pi Network daga sharrin mugaye masu kyashi da mahassada

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN