Wallahi Ko Kaffara Babu Watan Maulidi Yafi Watan Ramadana Daraja
Ɗan Ɗari kan tijjani ne dake bada wani cikekken jawabi wata Maulidi A nashi fahin ta.
Wallahi Ko Kaffara Babu Watan Maulidi Yafi Watan Ramadana Daraja –
A Cewar Rabilu Dauda Giwa kuma ya kara da cewa
MAULANMU SHEHU IBRAHIM ABDULLAHI NIASSE (R.A) Yana Cewa:
“NI Na Lura Duk Wata Halitta Ta Yi MAULUDI, Ba Ma Ga ‘Yan Adam Ba Kawai, Domin;
*. Katangar Kisra Ta Yi Mauludi Inda Ta Rarrawa Ta Tsage Saboda Haihuwar MANZON ALLAH(S.A.W).
*. Wutar Farisa Ta Yi Mauludi, Shekara Dubu Ana Hura Ta Amma a Lokacin HaihuwarSA(S.A.W) Ta Mace.
*. ‘Koramar Buhairata Sawata Ta ‘Kafe Saboda HaihuwarSA(S.A.W), Alhali Ana Zaton Ba Za Ta Ta6a ‘Kafewa Ba.
*. ‘Koramar Dabariyya Ita Ma Ta Yi Mauludi Inda Ta Kawo Ruwa a Lokacin HaihuwarSA(S.A.W), Alhali Ta Yi Shekaru Masu Yawa a ‘Kafe.
*. Taurari Sun Yi Mauludi Inda Suka Sauko ‘Kasa-‘Kasa a Daren HaihuwarSA(S.A.W).
*. Karagogin Manyan Sarakunan Duniya Sun Yi Mauludi Inda Suka Kife Saboda Haihuwarsa(S.A.W)”.
ALLAH YA ‘KARA MANA ‘KAUNAR MA’AIKI(S.A.W), YA ‘KARA MANA HIMMA CIKIN HIDIMAR SHUGABA(S.A.W) AMEEEEEEN
Daga Othman Muhammad