Wannan Shine Wasiyar da Abduljabbar ya aiko daga gidan yari inda yake neman lauyan da zai saya masa.
Wannan Shine Wasiyar da Abduljabbar ya aiko daga gidan yari inda yake neman lauyan da zai saya masa.
Fitaccen Malamin Islamar nan a Najeriya Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabbara ya fitar da sanarwar neman lauyan da zai tsaya masa a gaban Kotun ɗaukaka ƙara bayan Kotun shigar da ƙara ta yanke masa hukumcin Kisa a baya
A cikin wannan wasiƙara Abduljabbar yace yana son Lauyan da zai tsaya masa ya kasance ƙwararre wanda zai iya fitar dashi daga cikin halin tsaka mai wuya da yake ciki, kuma mai gaskiya saboda Lauyoyin baya sun cinye masa kuɗi a banza wasun su ma guduwa suka yi akwai wanda ya karɓi Naira Miliyan 10 wani kuma Miliyan 20 wani 2 sannan akwai ma Lauyan da ya karɓi Naira dubu 700 sun cinye masa kuɗi fiye da Naira miliyan 30