Labaran duniya

WASU SOJOJI ‘YAN FASHI SUN HARBE BABBAN MALAMIN MUSULUNCI

Wannan da ake gani a hoto Malamin addinin Musulunci ne, sunansa Sheikh Muhammad Goni Aisami

Ranar juma’a da ta gabata, Malamin yana kan hanya daga jihar Kano zuwa Gashuwa a jihar Yobe cikin motarsa kirar Honda 2006 model, ya iso kusa da barikin Sojoji na Nguru, sai wani Soja mai mukamin Lance Corporal sunansa JOHN GABREIL ya tareshi, ya roki ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji

Malamin sai ya daukeshi a mota suka tafi, suna cikin tafiya sun iso wani kauye da ake kira Chakama, sai Sojan ya fitar da bindiga kirar AK47 ya harbi Malamin harbi uku ya kashe shi nan take, sai Sojan ya kira wani abokinsa Soja mai suna ADAMU GIDEON yana aiki a rundiar Recca Battalion 241 akan yazo ya tayashi tafiya da motar Malamin, cikin ikon Allah sai motar taki tashi, a haka akazo aka kamasu

Sojojin da suka aikata wannan mummunan ta’addanci yanzu haka suna hannun hukumar Soji a garin Damaturu ana bincikarsu, sun tabbatar da cewa sun kashe Malamin ne kawai don su gudu da motarsa, abinda bincike kenan ya tabbatar ba barayi bane ko ‘yan Boko Haram suka kashe Malamin, sojoji ne kuma ba Musulmai ba إنا لله وإنا اليه راجعون

Yau inda wasu sojoji ne Musulmai barayi suka hallaka wani Malamin addinin da ba na Musulunci ba, da yanzu labarin nan sai ya isa majalisar dinkin duniya

Muna kira ga Maigirma Gwamman jihar Yobe, kayi amfani da karfin ikonka kabi kadin jinin wannan Malami da wasu ‘yan ta’addan sojoji suka zubar, ba mu yarda a bar binciken sojojin a hannun rundinar soji ba

Anyi jana’izar Malamin jiya asabar, ya samu dunbin jama’ar Musulmi da suka masa jana’iza tare da rakashi makwancinsa

Darasi anan shine, idan kana tafiya da mota ka kiyaye rage wa wanda baka sanshi ba hanya, musamman idan yana rike da jaka babba ko wani kaya, idan shi kadai ne zaka iya rage masa hanya, amma ka dubeshi da kyau, ka tabbatar a doke ba zai iya murdeka ba, sannan kar ka tsaya a wajen gari kace zaka saukar dashi

Muna rokon Allah Ya gafarta wa Sheikh Muhammad Goni, Allah Ya karbeshi a matsayin shahidi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN