Wata Budurwa ta fashe da kuka bayan takashe dubu tara a sufuri domin ganin saurayinta
Wata Budurwa Ta Kashe Naira Dubu 9 Kuɗin Mota Domin Ganin Saurayin Da Suka Haɗu A Midiya
Daga Aliyu Adamu Tsiga
Wata ƴar Najeriya ta yi kuka bayan ta kashe N9k a sufuri domin ganin saurayinta, yayin da shi kuma ya ba ta N1,300 bayan sun shafe kwanaki uku suna lalata.
Kafofin sada zumunta sun yi ta ce-ce-ku-ce tun bayan da wata ƴar Najeriya ta bayyana abin da ya faru da wani saurayi da ta je Legas domin ta ganshi wanda suka haɗu a soshiyal midiya.
A cikin sakon imel da matar ta aika wa ƙwararre kan hulɗar dangantaka, Joro Olumofin, ta bayyana yadda ta haɗu da wani saurayi a Instagram bayan alaƙarsu ta yi tsanani kuma suka yanke shawarar haɗuwa.
Ta bayyana cewa ta kashe N9k ne kuɗin sufuri har zuwa Legas domin ganawa da shi tare da yi mata alƙawarin ba ta kuɗi da kuma kwamfutar tafi-da-gidanka da saurayin ya yi mata.