Labarai

Wata Kotu A Najeriya Ta Ba Da Belin DCP Abba Kyari Dómin Alhinin Rasuwar Mahaifiyarsa

DA ƊUMI-ƊUMI: Wata Kotu A Najeriya Ta Ba Da Belin DCP Abba Kyari Dómin Alhinin Rasuwar Mahaifiyarsa

Wata babbar kotun tarrayya, ƙarƙashin jagorancin Justice Emeka Nwite, ta bayar da belin fitaccen ɗan sanda DCP Abba Kyari na tsawon sati biyu domin ya je yayi Addua’ar rasuwar mahaifiyarsa da kuma karɓar ta’aziya.

A ranar Talata ne 21/05/2024 lauyoyin Abba Kyari su ka yi roko ga kotun da ta saki Abba Kyarin ya je gida Maiduguri domin karban ta’aziya da Addua’a akan rasuwar mahaifiyar tasa.

Idan za ku iya tunawa an gurfanar da Abba Kyari a manyan kotun tarrayya guda biyu ne. Ɗaya a gaban Justice James Omotosho wanda shi ya bada belin Abba Kyari tun ranar 31/05/2023. Ɗaya Kotun kuma ta Justice Emeka Nwite ta riƙe shi.

Anma yanzu kuma shi ma Justice Emeka Nwite ya bayar da belin Abba Kyarin na sati biyu.

Wannan ya nuna cewa Abba Kyari zai iya fitowa daga gidan gyaran hali don ya je ya gana da yan’uwansa, abokan arziki da kuma karɓar ta’aziya akan rasuwar mahaifiyarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN