Wata Sabuwa: An gano wata laya mai dauke da sako daga lahira a Masar
Babbar Magana: An gano wata laya mai dauke da sako daga lahira a Masar
An gano wata babbar makabarta ta manyan sarakunan zamanin baya a Masar mai dauke da akwatunan gawa da kuma wata laya mai dauke da “sako daga lahira.”
Makabartar wadda ke kusa da birnin Minya a kudancin birnin Alkahira, ta fi shekara 2,000, kuma ana sa ran za ta sake shafe wasu shekara biyar din kafin a gama tone ta,
Ministan adana kayan tarihi Khaled al-Enany ya ce an samu akwatin gawa wanda aka yi da dutse guda 40 da kayan kawa da tukwanen kasa da abun rufe fuska na zinare.
Ya ce akwai wuraren da aka bunne mutane tun daga zamanin Fir’auna na farko zuwa fira’aunonin da suka biyo kusan shekara 300 kafin haihuwar Annabi Isa.
Ya shaidawa manema labarai cewa: ‘Wannan mafarin gano sabbin abubuwa ne. Nan ba da dadewa ba za mu kara wasu sabbin kayayyakin tarihi a Tsakiyar Masar.”
Shugaban masu binciken kayan tarihi Mostafa Waziri,ya ce an gano kaburbura takwas cikin wata uku da suka gabata, amma yana sa ran za a sake samun wasu da dama, BBC ce ta wallafa labarin tun a 2018
Ya kara da cewa: “An shirya cewa aikin tono zai shafe tsawon shekara biyar a wani kokari na gno duk abubuwan da aka binne a makabartar.”
Mr Waziri ya ce mafi yawan kaburburan na tsoffin masu bautar wani tsohon abun bauta na Masar ne mai suna Thoth.
An kuma gano wasu tulu hudu da aka adana wadanda suka yi kama da fuskokin ‘ya’yan wani tsohon abun bautarsu Horus.
Mr Waziri ya kara da cewa: “Suna kuma dauke da wasu bangarorin jikin mamatan. An yi wa tulunan ado da wani rubutu inda aka sanya sunan masu shi.”
Ya bayyana yadda aka yi wani dace mai ban mamaki na samun wata laya a jajibiren sabuwar shekara, wadda aka rubuta “barka da sabuwar shekara” a jikinta, da rubutun mutanen Masar na da.
Ya ce: “Wannan sako ne da aka aiko mana daga lahira.”
Four canopic jars, made of alabaster with lids bearing the faces of the four sons of god Horus, that were unearthed are displayed at the site of an ancient Egyptian cemetery, in Minya province, 245 km south of Cairo, Egypt.
A farkon wannan wata ne, masu bincike suna gano wani hubbare na wata tsohuwar malamar wurin bauta da ta mutu kusan shekara 4,400.
An kawata ta aka kuma adana ta cikin wani bango da aka yi wa fenti, da aka zana zana malamar cikin yanayi kala-kala.