Labaran duniya

WATA SABUWA: Takakawa bazasu shiga Aljanna ba- Inji Wani Babban Minista

WATA SABUWA: Takakawa bazasu shiga Aljanna ba- Inji Wani Babban Minista

Daga Hajiya Mariya Azare

Wasu kalamai da wani babban dan siyasa yayi sun jawo magan ganu saboda tsaurin maganan kamar yadda mutane suka tabbatar.

Labarin da muka samu daga jaridan aminiya ya shaida mana cewa ministan cikin gida na uganda, mista kahunda otafire ya shiga cikin tsaka mai wuya sakamakon wasu kalaman da yayi dake nuna cewa talakawa bazasu shiga aljanna ba.

A cewan ministan dai talakawan bazasu shiga aljanna bane saboda sukan da suke yima ubangiji wajen gabatar da korafe korafe kowane rana.

Ministan yayin jawabi a gun wani taron dalibai a kyenjojo, ya shaida musu cewa kadasu zargi ubangiji idan sun kasa amfani da daman daya basu na yakan talauci, inda ya umarce su dasu jajirce wajen samun arziki akan korafin da sukeyi kowane rana.

Mista otafire yace kukure ne mutane suyita gabatar da korafe korafe da kuma zargin ubangiji batare da tashi tsaye wajen yin ayyukan da zasu samar musu da kudade ba.

Ministan yace, wannan hali na sukan ubangiji da talakawa keyi shi zai hanasu shiga aljanna.

Wadannan kalamai sun haifar da cece kuce a kasar indiya wadansu malaman addinai da kugiyoyi suke zargin gwamnati da gazawa wajen samar da yanayi mai kyau ga talakawa zasu samu saukin halin kuncin da suka samu kansu.

Kasar uganda na daya daga cikin kasashen da suke da dimbin matasa da basuda ayyukan yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN