Labaran Kannywood

Wata Sabuwar Yadda Ake Zargin Jarumin Kannywood Baba Ari Da Dukan Malama Makaranta Islamiyya

Wata Sabuwar Yadda Ake Zargin Jarumin Kannywood Baba Ari Da Dukan Malama Makaranta Islamiyya

Wata Sabuwa Inji Yan Caca Yanzunan Majiyar Ta Samu Labarin Yadda Ake Zargin Baba Ari Da Dukan Malamar Islamiyya Kamar Yadda Shafin Daily Nigerian Hausa Suka Wallafa

Makarantar Ummusslama Islamiyya da ke a unguwar Mubi, Kofar-Nassarawa a Jihar Kano na zargin fitaccen ɗan wasan barkwancin nan na masana’antar fim ta Kannywood, Baba Ari da dukan wata malamar makarantar islamiyyar.

Hukumar makarantar na zargin Baba Ari da dukan malamar mai suna Safiyya Nasir bisa dukan ƴarsa da ta yi.

Freedom Radio ta rawaito cewa Malama Safiya Nasir, ta ce tana zaune a cikin Aji ta biya musu karatu, sai ƴar Baba Arin ta ke cin cingam tare da wata ɗalibar a kusa da ita.

Bayan kuma dama wani malami mai suna Malam Sulaiman yayi musu magana kan su daina cin cingam a aji. Saboda haka sai na ce ta biya karatun sai ta ki biya wa ni kuma sai na dauki Bulala da daki ta kusa da ita, amma ita Hafsa sai ta ce ba za’a dake ta ba, har mu ka yi sa’insa. Ina fara yi mata bulala sai ta zube a ƙasa wanwar da nufin ta tayar da Aljanu.

“Ina cikin tafiya ne sai ga mahaifinta ya zo, yana cewa, ke Hafsa waye ya doke ki, wacce malamar ce ta dake ki? Ana fada masa kawai sai ya janyo ni ya kifa min mari, ya fara taka bayana da takalminsa.”

Hakazalika hukumar makarantar ta ce ba za ta yarda ba sai ta ɗauki mataki

Freedom Radio ta rawaito cewa da a ka tuntuɓe shi a nasa bangaren, Ari Baba, yace ya yarda yayi kuskure, kuma ya amsa laifinsa, inda ya ƙara da cewa ya gana da mahaifan Malama Safiyya ya kuma bada hakuri.

Sai dai kuma Baba Aria ya yi rantsuwa da Allah cewa shi bai dake ta ba, inda ya ce gefen dankwalin ta kawai ya daka.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Munagodiyadasauraranmu dakuke akodayaushe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN