Labaran duniya

Yadda Aka Damke Wasu ‘Yan Camaroon Da Kokon Kawunan Mutane A Nijeriya.

An Damke Wasu ‘Yan Camaroon Da Kokon Kawunan Mutane A Nijeriya.

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa a Nijeriya, ta damke wasu mutane biyu ‘yan Kasar Kamaru da Kokon kawunan mutane za su siyar a Nijeriya.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana nasarar kama mutanen ne a ranar Alhamis din nan, inda ta ce ta cafke ‘yan kasar Kamarun biyu da zargin saida sassan jikin mutum bayan ta tarar da Kokon kawunan mutane tare da wasu kasusuwa a tare da su a yayin rutsa su da ta yi a garin Garware da ke cikin karamar hukumar Fufore ta jihar.

A yayin baje kolin wadanda ake zargi a gaban Manema Labaru, Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, SP Sulaiman Yahya Nguroje ya bayyana cewa mutanen biyu da aka kama bisa zargi masu suna Raji Silver da Nodji Kodji, sun kasance mazaunan garin Cholli na kasar Kamaru ne.

Kakakin ya kara da cewa, an yi nasarar damke su ne bayan da suka tsallako Nijeriya suka kawo wa wani dan Achaba mai suna Dauda Yakubu mazaunin garin Farang a karamar hukumar Fufore kokon kan domin saida masa, amma a wannan karon ya nuna masu shi bai da bukata.

Ya ci gaba da cewa, bayan haka ne suka shiga gari domin nemo wani mai siya, inda a nan ne a cewar Nguroje jami’ansu suka yi nasarar damke su a yayin da suke wani suke sintirin aiki.

SP Nguroje, ya bayyanawa manema labaru cewa, a yayin binciken duk wadanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa, inda suka ce lallai suna tono gawarwakin mutane ne sa’annan sai su ciri sassan da suke bukata su je su saidawa wasu mutane, inda suka ce shi ma Dauda sun ta6a saida masa Kokon kan a miliyan biyar biyar (5m) na kudin kasar Camaroon.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN