Labaran duniya
Yadda Aka Kama Matashin Da Yayi Fice Wajen Lalata Yan Mata Da Sunan Nema Musu Aiki
Wani mutum da ke yaudarar mata masu neman aiki yana yin lalata da su ya fada a komar jami’an tsaro
’Yan sanda a Bayelsa sun gano dan damfarar yakan yi sojan gona ne a matsayin jami’in gidan gwamnatin jihar, inda yake yaudarar mata tare da yi musu alkawarin aiki.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya ce asirin dan damfarar ya cika ne bayan daya daga cikin ’yan matan ta kai kara, aka cafke shi a unguwar Opolo da ke garin Yenagoa.
Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike gabanin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.