Yadda Akayi Liyafar Auren Aisha Humaira da Angonta Dauda Kahutu Rarara ayau
Yadda Akayi Shagalin Bikin Amarya Ayshatul Humairah Da Angonta Na Amana Alhaji Dauda Kahutu Rarara a Daren Jiya a Birnin Kano.
Taron Ya Sami Halartar Manyan Baki Irin Su Tsohon Gwamna Katsina Kuma Shugaban Hukumar TET FUND Na Kasa Rt. Hon. Aminu Bello Masari Da Gwamnan Jahar Gombe Kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Alhaji Inuwa Yahaya Da Kwamishinonin Jahar Katsina Da Kwamishinonin Jahar Gombe Da Kwamishinonin Jahar Jigawa Da Masu Bawa Gwamna Shawara Na Jahohin Jigawa Da Gombe Da Katsina.
Sannan Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Akan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu Ya Aiko Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bikin.
Karamin Ministan Tsaro Da Babban Ministan Taro Suma Duk Sun Aiko Da Wakilansu Wajen Shagalin Wannan Bakin.
Mataimakin Shugaban Sanatocin Nigeria 🇳🇬 Sanata Barau Jibrin Maliya Shima Ya Aiko Da Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bikin.
Sannan Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam Shima Ya Aiko Da Wakilinsa Wajen Wannan Shagalin Bakin.
Alhamdulillah Anyi Taro Lafiya An Gama Lafiya.
Allah Ka Dauwamar Da Zaman Lafiya Tsakanin Amarya Da Ango…🤲-🤲
Rabi’u Garba Gaya
Media Aide To Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara.