Yadda Bidiyon wanni dattijo Yana Karkada labbansa a TikTok ya Girgiza Duniya da Nishaɗi
Yadda Bidiyon TikTok Ɗin Wani Dattijo Yana Karkaɗa Laɓɓansa Ta Salo Na Musamman Ya Nishaɗantar Al’ummar a TikTok
Daga Haleemah Khaleed
Wani sabon shigar TikTok ya ɗauki hankalin mutane da dama yayin da ya saki bidiyonsa na farko wanda mutane da dama su ka nishaɗantu da shi a ranar 9 ga watan Satumban 2022. Nan da nan mutane su ka dinga kallo, Legit.ng ta ruwaito.
A shafin TikTok din dattijon, an ga bidiyoyi uku kacal, amma bidiyonsa na farko ya fi ɗaukar hankalin jama’a.
An ga yadda ya kwalmaɗa laɓɓansa na sama da ƙasa a wani yanayi mai nishaɗantarwa tamkar yana cin yaji.
Nan da nan mutane su ka bazama su na kallon bidiyon wanda akalla yanzu haka mutane fiye da miliyan ɗaya da rabi (1.5m) ne suka kalli bidiyon.
•Tsokacin Jama’a Ƙarƙashin Bidiyon
Tsokacin mutane daban-daban waɗanda su ka yi ƙarƙashin bidiyon:
Wata Sophie sophy tace:
“Bidiyo ɗaya ya saki, amma har mutanen ƙasashen waje sun san da shi.”
akua mawuli yace:
“Ina ƙasa ina kwasar dariya. Na zaci shawara zai ba mu ne.”
San Davi yace:
“Yadda ya zauna hankali kwance, kila zatonsa bai ɗora bidiyon ba.”
George Ofosuhene yace:
“Shiyasa na dena hawa TikTok da dare, ta ya za ayi in yi bacci yanzu.”
Wani user3390040882140 yace:
“Na natsu ina kallonsa, zato na shawara zai bayar.”
Dadai Bidiyon: