Labaran Kannywood

Yadda kasan ‘Bunsuru’ haka miji na yake idan ya ga mace wata Mata take bayyana halayen mujinta a Kotu

Yadda kasan ‘Bunsuru’ haka miji na yake idan ya ga mace wata Mata ta Koka a Kotu

Daga Aisha Yusuf

Kotun gargajiya dake Igando jihar Legas ta raba auren Isoboye Dominic da Christopher a dalilin zargin yawan neman mata a waje da Christopher ke yi.

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis alkalin kotun Koledoye Adeniyi ya ce ya warware kullin auren ne saboda hujjojin da aka bada sun nuna cewa Christopher ya auri Isoboye saboda kudin da mahaifiyar ta take da shi ne amma ba domin yana son ta ba.

Adeniyi ya ce cin zarafi, yawan fada da rashin kula da iyalinsa ya nuna cewa Christopher bai shirya aure ba balle ya zama Uba na gari ga ‘ya’yan su biyu.

Ya ce a dalilin haka ya raba auren. Christopher zai rika biyan Isoboye Naira 20,000 duk wata domin kula da kanta sannan da Naira 200,000 kudin diyya ta hannun kotu.

Adeniyi ya bai wa Isoboye ikon kula ‘ya’yan su biyu da suka haifa tare sannan Christopher zai iya ganin ‘ya’yan sa a wurin da shi da Isoboye suka amince su hadu.

Ya ce kotu za ta daure Christopher na tsawon watanni shida idan bai cika waɗannan sharudda ba.

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga Oktoba 2021 ne Isoboye ta Kai karan mijinta kotu inda take rokon kotun ta raba auren ta da Christopher saboda yawan neman mata da yake yi a waje.

Isoboye ta ce wata rana a otel ta kama shi yana lalata da wata mata amma ya kama ta ya yi mata dukan tsiya.

Ta ce Christopher baya kula da ita da ‘ya’yan su biyu sannan ga yawan duka da masifa da yake yawan yi mata.

Isoboye ta ce ta gaji da auren Christopher kuma ta roki kotu da ta bata izinin kula da ‘ya’yan su biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN