Labaran duniya

Yadda Na Kama Mijina Da Mahaifiyata Turmi Da Taɓarya Suna Jima’i

BABBAR MAGANA: Na Kama Mijina Da Mahaifiyata Turmi Da Taɓarya Suna Jima’i, Wanne Mataki Ku Ka Ga Ya Dace In Ɗauka? Cewar Wata Matar Aure

Wata matar aure da ke zama a jihar Gombe amma mijinta yana aiki a Abuja ta bayyana yadda da tsakar dare ta kama mijinta da mahaifiyarta su na lalata, kuma har ta gansu ta bar wurin ba su kula da ita ba.

“Tun da nake zaune da mijina, bai taɓa ɓata min rai ba ko kuma yayi min wani abu na musgunawa, amma a wannan karon kaina ya kulle sakamakon abinda na gane wa idanu na.”

“Mahaifina ya rasu, hakan yasa bni da wacce ta wuce min mahaifiyata. Bayan na haihu ne mahaifiyar tawa ta je gidana da ke Gombe don tayi makonni uku na zaman jego.”

“Dama kullum sai mijina ya bani fura, ashe yana sanya min maganin bacci a ciki, amma ranar da dubunsu za ta cika ban sha furar ba.

“Farkawata ke da wuya, sai ban ga mijina a gefe na ba, hakan yasa na yi tunanin ko ya shiga ban ɗaki ne, kasancewar ɗakuna biyu na kwana gare mu, sai na yanke shawarar komawa ɗaya ɗakin don na yi amfani da bayin.”

Shiga ta ke da wuya na ga mijinta da mahaifiyarta su na lalata, sai Ubangiji ya sanya man nutsuwa na lallaɓa na koma ɗaki na kwanta cike da damuwa.”

“Hakan yasa nake neman shawarar yadda zan ɓullo wa lamarin.” In ji ta.

~ IDON MIKIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN