Labaran duniya

Yadda Wani La’ananne Ya Yiwa Siyama Yà Mai Shekaru 3 Fyaɗe Har Ta Rasu

Yadda Wani La’ananne Ya Yiwa Siyama Yà Mai Shekaru 3 Fyaɗe Har Ta Rasu

Siyama ta rasu ranar Alhamis 29-09- 2022 kimanin karfe 4 na yamma a dalilin Fyade da wanda ake tuhuma wani Idi (Baba Idi) mai shekaru kimanin 40 zuwa sama, dake zaune a Lungun Alhaji Halliru a unguwar Gama, karamar hukumar Nassarawa ya yi mata ranar Talatar da ta gabata.

Kimanin kwana shida da ya gabata, Idi ya dauki Siyama zuwa dakinshi ya bata alewa inda ya yi lalata da ita kuma ya tsoratar da ita cewa in dai ta fadawa Abbanta sai ya kasheta da Almakashi kuma ya hadata da magen gidansu ta cinyeta (kasancewar ta mai tsoron mage) ta kwatanta mana yadda ya dora mata almakashi a wuya yace sai ya yankata da shi idan ta fadawa Abbanta.

Bayan ta shigo gida an cire mata kaya za ayi mata wanka aka ga jini yana fitowa daga jikinta, aka ce me ya sameta tace “Baba Idi ne yake mun wani abu yauma ya ciremin wando ya yi min ya bani alawa kuma yace idan na fadawa Abbana ze kasheni, Umma don Allah kar ki fadawa Abba”. Daga nan aka dauketa aka kaita asibiti inda likitoci suka tabbatar da ‘Penetration’ kuma suka fadi hanyoyin da za a bi a kula da lafiyarta.

Bayan jami’an tsaro sun kamashi an kaishi CID ana cikin bada statement aka fito dashi da ankwa, tana ganinshi ta rude da firgici tana cewa “Umma yace kasheni zai yi da Almakashi, me yasa ki ka fadawa Abba? Kasheni ze yi kuma zai hadani da mage” daga nan zazzabi ya kamata aka dawo da ita gida, har zuwa washe gari da ta rasu tana ta maimaita kasheni zeyi da Almakashi.

Yau kwanan Siyama uku da rasuwa sakamakon zalunci da cin zarafin da wannan la’anannen Allah ya yi mata, Allah ya gafarta mata yasa mai ceton iyaye ce, shi kuma Allah ya kare Al’umma da sharrin mutane irinsa yasa ya girbi abinda ya shuka.

Daga Bilya Abubakar Muhammad

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN