Labaran duniya

Yadda Wani Pasto ya Fito Kuru-Kuru Ya Bayyana Musulunci gaba Yake da Kiristanci

Gaskiya daya ce! Wani malamin addinin Kirista, Bishop Sam Zuga ya fito kuru-kuru ya fadi cewar addinin Musulunci gaba yake da Kiristanci, yana mai kafa hujjoji kamar haka;

An haifi Annabi Isa (AS) shekaru 571 kafin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) amma duk da haka addinin musulunci na goga kafada da Kiristanci a duniya.

Musulumi na amsa sunan Mohammed fiye da Kiristoci dake amsa sunan Emmanuel.

Musulumi na yin sallah biyar a rana amma da kyar kiristoci ke zuwa coci sau daya a sati.

Ya kara da cewar, Qur’an guda daya ne kuma cikin yare guda amma littafin injila (bibble) ya fi kashi 10 a cikin yaren Turanci kadai.

Musulumi kan iya yin sallah a kowanne masallaci kuma a ko ina amma mabiya addinin Kirista ba zasu soma shiga wata cocin ba saboda ba a irinta su ke ibada ba.

Idan har karbi addinin musulunci, babu mai tambayar ka masallacin ka, amma idan mutum ya zama Kirista dole sai ya zabi coci ko kuma ka tashi a tutar babu.

Ku kasance da shafin NAIJ.com Hausa domin karanta cikakken rahoton da kuma dukkan hujjojin da ya bayar a labaran mu na yammacin yau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN