Yadda Wani Tsoho ya Auri Jikarsa Kuma Yaki Sakinta Saboda Dadin yadda yake Jima’i da ita
Yadda mutumin ya cije akan kin rabuwa da jikarsa
Alhaji Musa Tsafe mai shekaru 47, ya cije akan kin sakin jikarsa wadda ya aura fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Mutumin wanda ke zaune a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara tare da iyalinsa, ya ce ba zai sawwakewa jikar tasa ba duk da an ankarar da shi a kan haramcin igiyar auren da aka kulla a tsakaninsa da ita.
Bayanai sun ce, matar mai suna Wasila Isah Tsafe mai kimanin shekaru 35, wadda jika ce ga babban yayan Alhaji Musa, ta haifa masa ’ya’ya takwas a tsawon shekaru 23 na aurensu.
Dadai Bidiyon
Sai dai wannan lamari da ya dauki wani sabon salo, ya kara jefa rayuwar ma’auratan cikin rudani, inda ma’abota sani na addinin Islama suka sanar da Masarautar Tsafe kan haramcin auren.
Shugabannin al’umma da malaman addinin musulunci da suka gayyaci ma’auratan domin su binciki lamarin, sun gano cewa auren ya saba wa koyarwar addini.
Hakan ce ta sanya Malaman suka shawarci Alhaji Musa a kan ya saki matarsa amma ya yi biris ya ce ba za ta sabu ba.
Wannan kuwa na zuwa ne duk da malaman sun halasta ’ya’yan da suka riga suka haifa, sai dai sun ce a yanzu da aka gano yadda lamarin yake, aure ya haramta a tsakaninsu.
Bayan ya kekashe ne aka mika lamarin zuwa Hukumar Hisbah da ke Karamar Hukumar Tsafe, wadda kuma nan da nan aka garzaya wata Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da a yanzu ta sanya 21 ga watan Yuli a matsayin ranar ci gaba da sauraron karar.
Ana tsaka da wannan takaddama ce, Alhaji Musa ya garzaya wajen Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai koken cewa wannan wata kitimurmura ce ta neman a sanya tsare-tsaren akidar ’yan Izala a cikin lamarin aurensa.
Sai dai daga karshe Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, ta raba auren wani mutum mai suna Alhaji Musa Tsafe wanda ya auri jikarsa shekaru 23 da suka gabata.
A baya dai hukumar Hizbah a Jihar Zamfara ta kai karar ma’auratan, kan bukatar kotu ta raba auren sakamakon saba wa dokokin Alkur’ani da litattafan musulunci.
Majalisar Shura ta karamar hukumar ta bukaci ma’auratan da su rabu bayan sun gano cewar auren ya saba wa dokokin addinin Musulunci.
Sai dai bayan watanni da aka sanar da ma’auratan haramcin auren nasu, sai suka ki rabuwa inda suka ce aurensu na kan hallaci.
Aminiya ta ruwaito cewa, ma’auratan sun haifi ’ya’ya takwas cikin shekaru 23 na rayuwar aurensu.
Da yake zartar da hukuncin, mai shari’a Bashir Mahe, ya ce bayan sauraron wadanda ake kara, kotu ta gano cewa auren da ke tsakanin ma’auratan ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.
Mai shari’a Bashir Mahe, ya ce auren ya saba wa aya ta 73 a cikin Suratul Nisa’i, da kuma umarni a shafi na 79 na Ashalul Madariki da shafi na 77 na littafin Ihkamil Ihkami.
Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan gazawar lauyoyin wadanda ake kara wajen shawo kan kotun da shaidu kan halaccin auren.
Sai dai alkalin ya ce wadanda ake tuhumar suna da damar daukaka kara idan har ba su gamsu da hukuncin ba.
Lauyan hukumar Hizbah ta jihar, Barista Muhammad Sani, ya ce ya gamsu da hukuncin da aka yanke tare da gode wa duk wadanda suka taimaka wajen nasarar da aka samu a shari’ar.
A baya dai mai shari’a Bashir Mahe, ya bayar da umarnin a kamo Wasila Isah bayan ta ki bin umarninsa na barin gidan aurenta zuwa gidan mahaifinta har sai kotu ta yanke hukunci.
Matar wadda a kokarin bijire wa yunkurin kama ta ne ya sa ta tsere.
Idan ba a manta Aminiya ta rawaito yadda magidancin ya dage kan cewar ba zai rabu da matarsa ba, yana mai cewa akidar ‘yan izala ake nema a kawo cikin lamarin aurensa.
Sai dai Shehun Malamin wanda shi ne jagoran Darikar Tijjaniya na Najeriya, ya tabbatar da maganar malaman ta cewa auren ya haramta, sai dai shi kuwa Alhaji Musa ya ce ya ji ya gani don kuwa shi da matarsa mutu-ka-raba.