Yadda Hatsarin Jirgin Ruwa A Jigawa Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane
Shugaban karamar hukumar Shehu Sule Udi, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi
A cewarsa, wadanda lamarin ya shafa na kan hanyarsu ta zuwa ziyarar jaje ne daga Dabi zuwa kauyen Siyango.
Udi ya ce an tsinto gawarwakin bakwai daga cikin 13 da suka nutse, yayin da sauran shidan kuma ba a gansu ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar hatsarin kwale-kwalen, ya ce an kaddamar da tawagar aikin ceto tare da taimakon masu ruwa da tsaki na cikin gida, inda ya kara da cewa an samu nasarar kwato mutane 7 a yayin da ake ci gaba da aikin ceto sauran shidan, a lokacin gabatar da wannan rahoto.
“Biyu daga cikin bakwai da aka dawo da su, likita ne ya tabbatar da mutuwarsu, yayin da sauran biyar, wadanda ke cikin mawuyacin hali, suna ci gaba da samun kulawar lafiya,” in ji shi.
Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa kwale-kwalen ya bugi wani abu kuma a hankali ya nutse yayin da wadanda ke cikin su suka nutse.
A halin da ake ciki, kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da kokarin neman gawarwakin sauran mutane shida da aka kashe.