Labaran Kannywood

Yan Mata Ku Yi Hattara Da Malam Alin Shirin Kwana Casa’in, Domin Rikakken Mazi*naci Ne, Cewar Wata Budurwa

‘Yan Mata Ku Yi Hattara Da Malam Alin Shirin Kwana Casa’in, Domin Rikakken Mazi*naci Ne, Cewar Wata Budurwa

Wata matashiya a jihar Kano ta gargadi mata ‘yan uwanta da kar su kuskura su yi mu’amala da Jarumin Kannywood Sahir Abdul wanda aka fi sani da ‘Malam Ali Na Kwana Casa’in’ tana mai cewa rikakken mazi*naci ne.

Budurwar wacce an kusa bikinta ta bayyana cewa a watannin baya kadan wata mu’amala ta ta’ba hada su, daga baya kuma ba ta san inda ya sami lambarta ba, sai ya biyo ta a WhatsApp ya bayyana mata cewa shi ne wane. Bayan sun gaisa ne sai ya fara bijiro mata da maganganun banza yana mai cewa ta daure ta amince ya yi zina da ita kamar yadda za ku ga kalaman jarumin a hoton screen shot din da aka dora wanda lambarsa ce da kowa ya san shi da ita.

Budurwar ta ki amince wa jarumin a yayin da ta bayyana masa cewa ta kusa zama mallakin wani, amma jarumin bai daina yi mata magiyar amincewa da shi su yi lalata ba, inda a karshe ta bayyana wa mijin da za ta aura abubuwan da jarumi Sahir ke yi mata.

Koda saurayin nata ya tuntubi Malam Ali don ya ja masa kunne ya kuma yi masa nasiha sai Malam Ali ya ce ya yi din, ya je duk abin da zai yi ya yi. Jin hakan ne ya fusata saurayin budurwar har ya bukaci jaridar KANO MEDIA da ta buga labarin ta kuma watsa kazaman kalaman batsa da Malam Ali ya yi don duniya ta gani ko hakan zai sa ya dauki darasi ya gyara.

Sai dai saurayin budurwar ya ce idan har karya ya yi wa Jarumi Malam Ali, to ya fito ya rantse da Alqur’ani ya karyata. Ko ya je Kotu su kuma za su je da wayar da Malam Ali ya turo kalaman batsar da ya yi daga nan duniya ta gani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN