Labaran duniya

Yan Sanda Kama Muji da Mata da ake Zargi da Kàśhè Nafiu Garondo a Kano.

Innalillahi Wa’inna Ilaihir 😭 Asiri Ya Tonu Yanzu-Yanzu. Yan Sanda Kama Muji da Mata da ake Zargi da Kàśhè Nafiu Garondo a Kano.

Labarin ba dadin ji: Dalilin da ya sa na kashe direban gidanmu – Inji matar aure Hafsat da rundunar yan sandan jihar Kano ta ɗamƙe bisa zargin kashe wani matashi a cikin gidanta a Kano

Ta ce ya hana ta yunkurin kashe kanta ne ya sa ta……

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Sirajo mai shekaru 24 bisa zargin kashe wani matashi mai suna Nafiu Hafizu da wuƙa kamar yadda zakuji daga bakinta a wannan Bidiyon.

GADAI BIDIYON ANAN

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane biyu a gaban manema labarai a ranar Juma’a.

Gumel ya ce Hafsat, wata mazauniyar Unguwa Uku da ke ƙaramar hukumar Tarauni, ta amsa laifin kashe mamacin ta hanyar daɓa masa wuƙa.

Ya ce an kama mijinta, Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma mai gadinsu Malam Adam mai shekaru 65 bisa laifin taimakawa wajen ɓoye gawar don ɓoye laifin kisan kai.

Hafsat ta shaida wa manema labarai cewa direban da ke zaune tare da su ya yi ƙoƙarin hana ta kashe kanta inda ya ƙwace wuka a hannunta.

GADAI BIDIYON ANAN

“Na ɗan yanke a hannuna sai ya ce in je in canza tufafina. Ina fitowa daga banɗaki na hango shi kwance sai na ɗauki wukar na daddaɓa masa,” inji ta.

A halin da ake ciki, mahaifin marigayin, Malam Hafizu Gorondo, yana zargin cewa ma’auratan sun haɗa baki ne don kashe ɗansa saboda wasu maƙudan kuɗaɗe da yake bin mijin matar.

Ya ce ɗansa ya shaida masa gazawar Dayyabu wanda shi ma abokin kasuwancinsa ne ya biya shi bashin N25m.

‘Yan sandan sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin bayan kammala bincike.

NAFI’U SAURAYIN HAFSAT NE: Ga yadda bincike ya tabbatar min kan labarin Nafi’u da Hafsat

DAGA M Inuwa MH

Nafi’u saurayin Hafsat ne da jumawa bayan Hafsat tayi aure shine suka ha’da Kai suka fara kasuwanci (Business) tare da Nafi’u Kuma Allah ya basu sa’a suka samu ku’di masu yawa har ita Hafsa ta bu’de Shago a zoo road, Hafsat da mijinta Dayyabu suna zama a wani karamin gida sai Allah ya bu’dewa mijin ya samu ya Gina Babban gida kafin domin su koma can da zama tare da matarsa, kafin nan ita Hafsat ta Riga ta ha’da mijin nata da Nafi’u sun saba harya zama kamar dan Uwa suna harkoki tare ba tare da mijin yasan abinda dake tsakanin matarsa da Nafi’u ba.

A lokacin da su Hafsat za su tare a sabon gidan su shine tace dole sai dai a koma Sabon gidan tare da Nafi’u haka Kuma akayi dole mijin ya amince ance Yana tsoronta kasancewar ta fishi ku’di.

Ana haka ne Nafi’u bashi da lafiya Kuma Already ya Fa’dawa Iyayensa cewa Yana da Ubangida a Kano ko da Iyayen Nafi’u suka zo Kano daga bauchi sai Nafi’un ya gabatar da Iyayen nasa ga Dayyabu mijin Hafsat amatsayin maigidan sa ne na kasuwanci, ba kowa yasan cewa Nafi’u saurayin Hafsat bane sai abokan Nafi’un da Kawayenta na kusa, ana zargin Yaron da Hafsat ta Haifa Dan Nafi’u ne domin suna kama sossai.

Ance ko Ina Hafsat za ta tafi tare suke tafiya da Nafi’u har Umrah Kuma mijin Yana kallo ba tare da yace komai ba.

Dalilin wannan rigima da ya sa Hafsat ta Kai kashe Nafi’u shine Nafi’un ne ya Fa’dawa Hafsat cewa zai yi aure ya samu wata matar aure tun lokacin shine ba a sake zaman lafiya ba tsakanin Hafsat da Nafi’u.

Allah ne ya taimakawa mijin Tabbas da shine zai kasance Gawa bisa wannan Dalilin soyayya Dake tsakanin Nafi’u da Hafsat Yanzu dai Hafsat ta kashe Nafi’u, Allah ya jikansa da rahama, jama’a don Allah a kiyaye dokar Allah a zaman aure idan ba haka Bala’i zai Cigaba da faruwa tsakanin Al’ummarmu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN