Yanzu yanzu ƴan sanda suka cafke wani mai katin zaɓe guda 101 a jihar Sokoto
Yanda ƴan sanda suka cafke wani mai katin zaɓe guda 101 a jihar Sokoto.
Daga Shamsu S Abbakar Mairiga.
Yan sandar jihar Sokoto, sun kama wani mutum mai suna “Nasiru Idris” a ƙaramar hukumar Sabon-Birni wanda yake da katin zaɓe har guda 101 wanda bana saba.
Kwamishinan ƴan sandar mai suna “Mr Usaini Gumel” yatabbatar da aukuwar lamarin. kana yace mai laifin ankama sa ne a 10, “October” a cikin ƙaramar hukumar ta Sabon-Birni na jihar Sokoto.
Gumel yakara da cewa, “akwai yiwuwar masu katukar zaɓen ba kawai daga ƙaramar hukumar Sabon-Birni Suke ba, zai iya yiwuwa, akwai na wasu jihohin, saboda bazamu iya binciko sahihan masu katin ba”
Kwamishinan yayi kira ga mutane, musamman wa’inda katin su ya ɓace. ko sun manta inda suka saka, to su zo babban ofishin ƴan sandar domin dubawa.
Kwamishinan ya kuma cewa “rundunar ƴan sanda zasu mai da katukan zaɓen ga ofishin hukumar zaɓe wato (INEC).