Uncategorized
YANZU-YANZU: Daga bana Najeriya za ta daina shigo da man fetur daga waje– inji Kyari
YANZU-YANZU: Daga bana Najeriya za ta daina shigo da man fetur daga waje– inji Kyari
Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewa daga ƙarshen shekarar nan ta 2024 Najeriya za ta daina amfani da man fetur din da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje,
Ya ce za a koma amfani da man da aka tace anan gida Najeriya wanda hakan zai jawo man yayi arha sosai tunda dama man yana yin tsada ne sakamakon tashin Dala idan an je sayo man daga ƙasashen waje za a shigo dashi Najeriya.