Labaran duniya

Yanzu-Yanzu Davido Yayi Martani akan Masu Cewa Yaci Mutuncin Addinin Musulunci

Yanzu-Yanzu Davido Yayi Martani akan Masu Cewa Yaci Mutuncin Addinin Musulunci.

A safiyar yau ne da Mawakin Kudancin Najeriya Davido yayi Martani akan wani Bidiyo da yasake a jiya a shafinsa na Twitter wanda a cikin Bidiyon ana wasa da Sallah ganin yadda suke Rawa a Cikin Sallar.

Mawaki dai Yayi Bayani Dalla Dalla kamar haka:

GADAI BIDIYON ANAN 👇

PLAY ▶️

Davido ya Bayyana kamar haka

Kafin kayi tsinuwa, ka nemi gaskiya:
Davido ba shi ne yayi wakar Jaye Lo a Masallaci ba, wani Musulmin mawaki ne mai suna Olamilekan Emeka Taiwo (Wanda akafi sani da Logos Olori.

Kuma a iya fahimtarsa da yadda yaga su na yin addini a kasar yarabawa ya dauka cewa zai iya aikata irin wannan danyen aikin a kokarinsa na ya nuna cewa, komai ya samu na arziki daga Allah ne. Kamar yadda za ka ji yana ambaton ALHAMDULILLAH a cikin wakarsa.

Kuma Davido ya saka wakar ne saboda shi wannan Musulmin mawaki, Logos Olori, yana cikin mawaka masu tasowa da Davido yayi alkawarin zai tallatasu domin su samu daukaka. Kuma abin da yayi kenan.

Don haka ba magana ce ta tsinuwa ba, magana ce ta mu musulmi mu tashi tsaye wajen kokarin fahimta da fahimtar da addininmu, musamman a yankin kudancin Nigeria.

Domin da mun taimaki Logos Olori ya san addininsa da hakan bai faru ba.

Daga Arewa Buzz

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN