Labaran Kannywood

Yanzu Yanzu Gwamnatin Nijar ta Chafke 442 da Safara’u Bayan Rawar Iskanci sukayi a Wannan Bidiyon

Yanzu Yanzu Gwamnatin Nijar ta Chafke 442 da Safara’u Bayan Rawar Iskanci sukayi a Wannan Bidiyon

ALLAH DAYA GARI BAMBAN: Yayin Da MR 442 Da Su Ola Of Kano Suke Sharholiyarsu A Nijeriya, A Jamhuriyar Nijar Kuma Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro Har An Tura Su Gidan Kaso

Fitaccen mawakin Hipop dinnan wanda aka fi sani da Mr_442 tare da abokin aikin sa Ola Of Kano, sun hadu da fushin hukuma a jamhuriyar Nijer bayan da suks aikata laifi mai girma.

Ɗaya daga cikin makusantan mawakin Murja Ibrahim Kunya ce, ta bayyana haka a shafin ta na TikTok.

Murja ta bayyana cewa tuni an aike da Mr 442 da abokin aikin shi zuwa gidan gyaran hali a Jamhuriyar Nijar tare da tarar aƙalla naira milyan goma kowannen su.

Murja ta bayyana irin laifin da suka yi inda tace, tunda farko mawakan sun yi yunkurin yin fasfo ne a Jamhuriyar Nijer, lamarin da ya zama babban laifi ga duk wanda ba dan kasar ba.

Mawakan biyu sun yi yunkurin yin fasfo din ne da niyyar samun damar haurawa kasashe da dama, duk da sun san cewa hakan babban laifi ne, inda suka yi aski da niyyar gujewa lamarin don kada a gane su yayin, yin fasfo din, saidai kasancewar su sanannu hakan ya sa aka gane su tare da kama su.

Bayan da aka gano su an kama mawakan tare da kaisu gidan yari, wata majiya ta bayyana mana cewa wannan abinda sukai laifi ne babba a Nijar wanda zai iya sawa ayi musu hukuncin shekaru 6 kowanne a gidan yari.

Idan dai ba’a manta ba Mr 442 ya shahara ne a Kafafen watsa labarai tun bayan haɗuwar su da Safara’u ta cikin shirin gidan Kwana Chas’in wato Safaa.

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN