Kannywood

YANZU-YANZU: Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri

YANZU-YANZU: Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 domin a tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, Rarara ya jajantawa Gwamna Babagana Zulum, Da mai martaba Shehun Barno a yayin ziyarar da Ya kai musu.

Sannan Rarara ya ƙara jajantawa al’ummar jihar, musamman waɗanda suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwan.

A yayin ziyarar jajen, Rarara ya samu rakiyar Hajiya Aysha Humaira, Dak Abdullahi Al-Hikimah, Alan Waƙa, da Onarabul Auawal Ahmed Bakori da sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN