Yanzu Yanzu Sojin Sama Sun Hallaka Shugaban Ƴan Bindiga Ali Dogo Da Wasu 30 A Kaduna
Sojin Sama Sun Hallaka Shugaban Ƴan Bindiga Ali Dogo Da Wasu 30 A Kaduna
Sojojin Najeriya sun kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga a jihar Kaduna, Ali Dogo, da mayakansa 30, kamar yadda PRNigeria ta rawaito.
An bayyana cewa, an kashe Dogo, wanda aka fi sani da Yellow, tare da ‘yan kungiyarsa, sakamakon harin da jiragen yakin rundunar sojin sama su ka kai a karshen mako.
Da ta ke tabbatar da tashin bama-baman kan Yellow da mayakansa, wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa fitaccen shugaban ‘yan bindigar, da ‘yan ta’addansa sun gudu daga jihar Neja zuwa wani gidan Alhaji Gwarzo da ke Yadi a Ƙaramar Hukumar Giwa domin tsira da rayukansu, sakamakon ci gaba da ruwan bama-bamai da jiragen NAF suka yi akan maɓoyarsa a Neja a kwanan nan.
Majiyar ta ce: “Abin takaici ga Yellow da mayakansa, yayin da su ke cikin taro, jirgin NAF ya kai hari gidan Alhaji Gwarzo, wanda ya sa duk wanda ke cikin ginin ya hallaka su ciki har da Yellow din”.
A halin da ake ciki kuma, PRNigeria ta kuma tattaro cewa an kai hare-haren bama-bamai a rana guda kan ‘yan ta’adda a wani wuri mai nisan kilomita 33 Arewa maso yammacin Mando a Kaduna.
“Bayan bayanan sirri na shugabannin ‘yan ta’adda da sojojinsu da ke taruwa a karkashin bishiya a wurin taron, an kashe ‘yan ta’adda da dama,” kamar yadda wata majiya ta NAF ta shaida wa PRNigeria.
Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF, ya tabbatar da nasarar harin jiragen saman, inda ya ce, “Rundunar sojin sama bisa umarnin shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, za ta ci gaba da kai hare-hare kan wadannan miyagu tare da hadin gwiwar jami’an tsaro. Bangaren kasa da sauran hukumomin tsaro domin kawar da yankin na hadin gwiwa da ma yankin Arewa maso yamma gaba daya daga ayyukan ta’addanci da sauran ayyukan ta’addanci”.