Labaran duniya

Yanzu Yanzu Yan Boko-Haram Dubu Bakwai sun Mika Wuya

Boko Haram dubu 7 sun mika wuya, an kuma ceto wasu ‘yan matan Chibok uku a borno

Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya ce sama da mahara 79,000 da suka hada da mayaka da wadanda ba mayakan ba ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya a Maiduguri, a cewar majiyar Yola 24

A cewarsa, hakan ne ya sa ake bukatar karin sansanoni a Maiduguri domin karbar tubabbun da aka ware domin zakulo maharan da wadanda ba mayakan ba.

A halin da ake ciki, babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Waidi Shuaibu, ya bayyana cewa a cikin wa’adin da ake yi, an kuma ceto wasu ‘yan matan Chibok uku.

‘Yan matan da aka gano su ne Falmata Lawan, Asabe Ali da Jinkal Yama, wadanda sunayensu ke a lamba ta 3, 12 da 20 a jerin ‘yan matan Chibok da aka sace.

An kubutar da ‘yan matan daban-daban a yankin Bama a ranar 30 ga Agusta, 1 ga Satumba da 2 ga Satumba bi da bi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN