Labaran duniya

Yanzun nan nayi Mafarkin Queen Elizabeth tana Shakatawa a Cikin Jannatul firdausi

BOKO AQIDAH KENAN

Hakika ban taba tsammanin Adamu Garba haka akidarsa take ba, wannan itace akidar ‘yan boko aqidah, Inter-faith, Feminist da Atheists

Amma shin Adamu Garba wa yake son ya burge? kowa ya san amsar, amma duk wanda yayi imani da Qur’ani Littafin Allah ya san matsayin son wadanda basu yadda da Kadaituwar Allah ba, musamman aya ta karshe da take cikin Suratul Mujadala

Don Allah duk wani dan boko akida da yake kauna ko so ko jibintar lamarin al-kuff@ru yaje ya samu Malami ya masa cikakken bayani akan wannan aya ta karshen Suratu Mujadilah wanda ta sauka akan wani Sahabin Annabi (SAW) da ya kattala Mahaifinsa a fagen yaki:
لَّا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُولَٰئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ

Allah Sarki rayuwa, sai na tuna lokacin zanga-zangar ENDSARS da wakilan IPOB suka taso Adamu Garba a gaba kamar zasu cinyeshi, har sukayi reporting application dinsa dake kan Google Playstore Google suka cire application din

Haka muka taso muka dinga bashi kariya tare da yunkurin daukar masa fansa, a lokacin sai da mutanen IPOB sukayi reporting Facebook account dina Facebook suka dakatar da ni na tsawon wata guda, ban san haka akidarsa take ba da ban bashi kariya ba

Muna rokon Allah Ya shiryar damu hanyar tsira duniya da lahira

Kamar Yadda Ya wallafa a Shafinsa na Twitter

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN