Yau Shekara 14 Da Rasǔwar Tsòhon Shugabañ Ƙasa Umaru Musa Yar’adua
BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 14 Da Rasǔwar Tsòhon Shugabañ Ƙasa Umaru Musa Yar’adua
CIKAKKEN TARIHIN RAYUWAR TSOHON SHUGABAN KASAR NAJERIYA, ALLAH MUSA YAR’ADUA
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Daga Comr Nura Siniya
Shúgaba ƙasa na farko a mulkin farar hula da akayi a tarihin Nàjeriya mai tausayi mai ƙishin talaka mai tsantsini da dukiyar talaka da son ganin al’umma taci gaba.
Abinda ya ƙara bani sha’awa da marigayi Yar’adua shi ne lokacin da yake neman a zabe shi bai fito yayi ma ƴan Nàjeriya alƙawuran ƙarya ba wanda yasan bazai iya cikawa ba. sai dai ya fito da tsarin 7-point Agenda ta yadda ya ƙudurci sauya fasalin Najeriya don ganin talaka ya samu sauƙin rayuwa da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa
‘Yar’adua ya zo da manufofi masu kyawan gaske inda ya fara inganta albashin ma’aikatan gwamnati da albashin jami’an tsaro da ƙara inganta alawus na matasa masu ɓautar ƙasa NYSC da suka kammala karatun jami’a tare da kawo ƙarshen rikicin tsagerun yankin Naija Delta ta hanyar sasanci domin Samar da haɗin kai tsakanin ƴan ƙasa da cigaban ƙasa mai ɗorewa.
Bayan nan shine shugaban ƙasa na farko da ya bayyanawa duniya abinda ya mallaka tare da ragewa kan shi Albashi tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya.
A zamanin mulkin Ƴar’adua talaka ya samu sauƙin rayuwa yasha jar-miya inda ya riƙa sayen kayayyakin masarufi cikin farashi mai sauƙi:
-Litar fetur N65
-Shinkafa N6,000
-Buhun fulawa 3500
-Buhun Sikari N6500
-Buhun Taki N2500
-Man girki N2500
-Litar kalanzir N50
-Litar Diesel N110
-Kujeran Makka N600,000
-Ƙwalin Indomie N850
Haƙiƙa ƙasar mu Najeriya ta canza bayan mutuwar tsohon shugaba Ummaru musa ƴar’adua tunda gashi muna ɗanɗana kuɗarmu a yanzu.
Lallai da Allah yayi ma wannan Shugaba tsawon rai toh da yankin arewa a yanzu ya samu gagarumin cigaba.
A ƙarshe muna rokon Allah ya yafe masa kurakurensa ya ƙara kawo mana wasu Shuwagaban nin masu ƙishi da ƙaunar talakawa irin shi waɗanda zasu mutu a rubuta sunan su da ɗanyen zinari a tarihin Najeriya.