Zaben 2023: Da dumi dumi Masu Hangen nesa sun Hango wanda zaici zabe a 2023
ZABEN 2023: Atiku, Tinubu, Kwankwaso, Peter Obi, Wa Ya Kamata Mu Zaba?
Daga Comr Abba Sani Pantami
Ku fara daurewa ku karanta sharhi da bincike na akan manya daga cikin masu neman shugabancin kasar.
Amma fa ku sani wannan bincike nane ba lallai kaima yayi dai-dai da bincikenka ko sharhin ka ba.
Ga binciken kamar haka;
KWANKWASO: Idan har kishin Arewa zaka yi ko kake yi kuma kana son saka kishin yankin a cikin siyasa to Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso zaka zaba a matsayin dan takarar shugaban kasa, domin a dukkan alamomi da suka bayyana yafi kowane dan takara kishin Arewa, sai dai wasu suna ganin zaben Kwankwaso kamar asarar kuri’a ne a wurin su dalilan su kuwa sune;
Abunda ya fara bayyana a zahiri Kwankwaso baida kudin da zai iya kashewa al-ummar Najeriya har ya jawo hankalin su da su zabe shi, duba da yanzu siyasar ta koma ta jari hujja dole komai sai da kudi, gashi kuma jam’iyyar shi karama ce ba ta rike da madafun iko koda na jiha guda a fadin kasar.
Dadi da kari wasu na ganin Kwankwaso yana matukar samun nakasu a cikin siyasar shi na rashin goyon bayan manyan ‘yan siyasar Najeriya, hakan ya samo asali ne ta yadda bai yadda ya dukar da kansa akan wani ba, shi kullum shine jagora sai dai a bishi badai yabi wani ba, wasu na alakanta hakan da girman kai.
TINUBU: Idan har kishin Addinin Musulunci zaka yi ko kake yi kuma zaka saka kishin Addini a cikin siyasa to Bola Ahmad Tinubu zaka zaba, dalili kuwa shine ya dauko mataimaki musulmi wanda hakan yasa kungiyoyin Addinin kirista suke ta sukarshi da nuna za su fito su gwabza da musulmai wanda zuwa yanzu hakan ya fusata musulmai da dama kuma sun kudiri aniyar lallai sai sun zabi Tinubu duk da sunsan dan takarar baida cikakkiyar lafiya ta jiki.
Duk da haka mutane da dama suna ganin cewa musuluncin ‘yan siyasar Najeriya ba shida wani amfani ga musulman Najeriya, don haka su babu ruwansu da addini wanda ya chanchanta kawai zasu zaba.
ATIKU: Duk wani mai kishin jam’iyyar PDP da wasu daga cikin wa ‘yanda APC ta fusata zas