Labarai

Zulum ya jagoranci rusa gidajen karuwai da Hotel 153 a jihar Maiduguri Borno State

Zulum ya jagoranci rusa gidajen karuwai da Hotel 153 a Maiduguri.

Hakan ya biyo bayan da karuwai da bata suka kashe wani dan sanda a Jami’ar.

Gaskiya Ran gwamna Zulum ya bace matuka kamar yadda zaku gani a Cikin bidiyon.

GADAI BIDIYON

PLAY ▶️

 

Baba gana umar zulum ya ba da umarnin rusa gidajen karuwai da kwace filayensu wanda Dalilin da yasa shine Yan iska za su dawo cikin lunguna kenan sai kuma ka ji ana cewa an yi fy*de a nan da can. Ya kamata masana halayyar zaman jama’a (Sociology) su dinga yi wa mahukunta bayani.

GADAI BIDIYON ANAN 👇

PLAY VIDEO

Sai da Wasu abubuwan suna bukatar “trade-offs” ne. Dole sai dai a hakura da wani laifin don kada a fada wani laifin. Shi yasa ake cewa “irtikaab akhaffud dhararain” a Usulu. Idan rufe karamin laifi zai janyo wani babban laifin, to hakura ake a bar karamin. Rufe gidan karuwai zai janyo kwararar yan iska cikin lunguna kuma hakan sai ya fi illa fiye da barin gidan karuwan.

Zamanin “Lockdown” da aka rufe gidajen yan iska, a lokacin aka samu yawaitar fy*ade fiye da kima saboda an rufe gidajen karuwan da za su je su yi. Shi kam iskanci ba za a taba dainashi ba har duniya ta nade. Tun daga zamanin Annabawa, sahabbai da tabi’ai, ba a taba lokacin da ba yan iska ba. Don haka a san yadda za a lallabashi shi ne sauki ba wai a ce dole sai an hanashi baki daya ba, don wallahi ba zai taba hanuwa ba ko me za a yi.

Yanzu wannan hukunci da na san za a yi ta yaba masa, zai bude wasu hanyoyin iskancin ne manya. Don dai gwara mutum ya biya ya yi iskanci akan ya dawo lunguna ya lalata yara kuma wasu su kwaikwayi dabi’unsa. Wadannan abubuwan duk masana Sociology sun sani. Amma wanda yake wa’azi da tunanin “idealism” ba zai gane me ake fada ba sai ya faru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Kalli Bidiyon Anan

X
KALLI BIDIYON ANAN